Buhari zai kammala 2nd Niger bridge – Fashola
-Ministan wutan lantarki, ayyuka da kuma gidaje, Babatunde Fashola ya nanata wa gwamnatin tarayya cewa ta yunkura dan ganin ta kamala, ginin 2nd Niger Bridge da sauran manyan ayyuka a jihar Anambra
-Ya bayyana aikin 2nd Niger Bridge a matsayin daya daga cikin manyan ayyuka da ya rataya akan gwamnatin tarayya
-Ya ce hanyar zai kawo inganci da kuma hanzarta ci gaban tattalin arziki, sufuri, da kuma siya da siyarwa a fadin kasar lokacin da aka kamala.
Fashola da Buhari
Ministan da ke kula da al’amarin wutar Lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ba yan’Najeriya tabbacin cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin kamala kwangilar 2nd Niger Bridge.
Fashola ya ba da tabbacin a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, a Onitsa, jihar Anambra, inda ya je lura da ci gaban da aka samu akan ginin 2nd Niger Bridge da wasu manyan ayyuka, Daily Post ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Minista ya ce tsare-tsare na kan hanya domin sabonta kasar
Fashola ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata biya diya ga duk wanda aikin ya shafi filin sa. Ya yi kira ga al’umman guraran gurin da ake ayyukan da kada su kawo katsalandan ga ci gaban aikin da ake yi.
A wata ci gaba, Babatunde Fashola ya bayyana yawan rashin wutar lantarki da kasar ta fuskanta kwanan nan, a matsayin sakamako na yawan hare-hare da wasu yan bindinga suka kai ga bututun mai a yankin Niger Delta.
The post Buhari zai kammala 2nd Niger bridge – Fashola appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.