Ibrahimovic naso ya koma Manchester United (Karanta dalili)
Wakilin dan kwallon kafan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic Mino Raiola ya ce yana so ne ya koma kulob din Manchester united don ramuwar gayya ga Pep Guardiola.
Ibrahimovic, Guardiola da Mourinho
A cikin watan Febreru da ya wuce ne dai Ibrahimovic din ya bayyana sha’awar sa ta komawa kasar Ingla da buga kwallo inda kuma ya bayyana kulob din Manchester a matsayin inda yake son zuwa. “E tabbas kulob din Manchester ya nuna ra’ayin sa kan shi, amma muna jira ne muga yadda zata kasance”. Inji wakilin nasa.
Yanzu haka dai ana rade radin cewa har ma ya amince da kwantaragin shekara daya da kulub din. Shi dai Ibrahimovic din bai taba boye tsananin gabar sa ga Guardiola ba.
A wata fira da yayi da gidan talabijin din CNN ya ce: “Ta fannin horaswa dai Guardiola ya iya amma ba mutum bane mai kima a idona. Ba abun da zan ce game da shi”.
Shi kuwa wakilin nasa yace: “Ina tunanin yana so ne ya rama abunda yayi masa ne a baya.” “Kuma nima dai kamar yadda Zalatan din yace to nima baya burgeni kwata-kwata. Ni ban ma yadda ya iya horas war ba.” Ibrahimovic din dai ya share tsawon shekaru 4 a PSG ta kasar Faransa.
The post Ibrahimovic naso ya koma Manchester United (Karanta dalili) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.