Gwamnatin, tsagerun Neja Delta sun cimma yarjejeniyar
Gwamnatin Najeriya tare da tsagerun Neja Delta sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta har na tsawon kwanaki 30.
Tsagerun Nija Delta
An dai cimma wannan yarjejeniyar ne saboda aba shugaba Buhari damar bayyana cikakken shire-shiren sa game da yankin na su, kamar dai yadda jaridar Thisday ta ruwaito. Duka bangarorin biyu dai sun cimma wannan yarjejeniyar ne satin da ya gabata lokacin da tawagar gwamnatin tarayyar karkashin jagorancin karamin ministan mai Dr. Ibe Kachikwu ta ziyar ci yankin inda ta kuma tattauna da wakillan tsagerun da kuma gwamnatin jihohin Bayelsa da Delta.
KU KARANTA: EFCC sun dirar ma Ortom
Wata majiya kuma ta ruwaito cewar ita dai yarjejeniyar an cimma ita ne ta bayan gida tsakanin karamin ministan da tsagerun inda ya nemi a ba gwamnatin ta shugaba Buhari wani lokacin don a samu damar ciyar da yankin gaba a kuma shika masu wasu sharuddan nasu.
“Idan ma masu sauraro zasu lura zasu ga cewar yan kwanakin nan ba’a fasa bututun mai ba. Wannan bai rasa nasaba da yarjejeniyar da aka cimmawa.” In ji majiyar tamu.
Majiyar tamu kuma ta cigaba da zayyano bukatun na tsagerun da suka hada da basu damar. Kula da da yawan albarkatun yankin, karin kudin shirin yafiyar da akeyi, kara kaimi wajen shirin tsaftace yankin sannan kuma da karin kudi wajen tabbatar da jami’a babba a yankin da dai sauransu.
Majiyar ta kara da cewa hare-haren basu rasa nasaba da yadda aka cire ginin jami’ar daga cikin kasafin kasar na 2016 daga ma’aikatar sufuri wadda Chibuike Amaechi yake jagoranta. Kafin dai wannan tsagaita wutar na kwanaki 30, gwamnatin Najeriya ta umurci sojin ta da su janye daga filin daga har na tsawon mako 2.
Su kuwa tsagerun har a lokacin su fito sun dauki alhakin wasu hare-hare da dama a kan bututun man na gwamnatin tarayya wanda hakan yayi matukar kawo wa kasar nan cikas wajen samun kudaden shiga da kuma wutar lantarki in aka ruwaito cewa kasar na asarar kusan gangar mai har miliyan 1.4 duk rana.
A cikin satin da ya gabata ne dai gwamnatin tarayyar karkashin jagorancin Dr Ibe Kachikwu suka ziyarci yankin na Neja delta da jihohin Bayelsa da Delta sannan kuma da inda aka kebe don gina Jami’ar da garin Warri.
The post Gwamnatin, tsagerun Neja Delta sun cimma yarjejeniyar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.