Yanzu-yanzu: An dakatar da shari’ar Saraki da Ekewremadu
Karar da gwamnati ta shigar tana tuhumar shugaban majalisar dattijai da Mataimakin sa Bukola Saraki da Ike Ekweremadu kan gurbata kundin tsarin majalisa wanda a kai gaban kotu ya tsaya sakamakon rashin mika takardar sammacin da ba’a yi wa wadanda ake tuhumar ba.
Saraki-Ekweremadu
Su dai wadan da ake tuhumar shugabannin majalisar Saraki da Ekweremadu zasu gurfana ne a gaban kotun bisa zargin gurbata tsarin mulkin majalisar na 2015. Gwamnatin tarayya ta hannun ministan shari’a kuma babban lauyan kasar ne dai ta shigar da karar inda take tuhumar Saraki da Ekweremadu tare da magatakardar majalisar Alhaji Salisu Maikasuwa da mataimakin sa Mr. Benedict Efeturi.
Tuni dai wadan da ake tuhumar suka karyata laifin da ake tuhumar su da shi din inda Ekweremadu ya bayyana cewa shi bashi da sannu a cikin bada kalar. Wani labari kuma mai kama da wannan shugaban majalisar dattijan Saraki zai cigaba da bayyana a gaban kotun da’ar ma’akata watau Code of Conduct Tribunal (CCT) inda ake shari’ar sa kan bayyana bayanan karya yau din nan talata 21 ga wata.
The post Yanzu-yanzu: An dakatar da shari’ar Saraki da Ekewremadu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.