Akwai rashin hankali cikin san rai yan majalisa – Sagay
– Farfesa Itse Sagay ya siffanta yan majalisan tarayya a matsayin yan son zuciya.
– Ya ce neman ma kansu fenshon kare rayuwa ya nuna kawai kan su suke wa aiki.
– Ya ce Bukola Saraki na amsan fensho a matsayin tsohon Gwamna kuma yana bukatan kari.
farfesaitse sagay
Shugaban kwamitin baiwa Shugaban kasa shawara akan yaki da rashawa, Farfesa Iste Sagay yayi turr da samarwan kariya da fenshon kare rayuwan da ake yunkurin yi ma shugabannin majalisa. An yi samarwan bada kariya da fensho wani taron Senatocin kwamitin kundin tsarin mulki da akayi a ranar asabar 19 ga watan Yuni a Jihar Legas. Samarwan ta kunshi baiwa Shugaban majalisan dattawa, mataimakin Shugaban majalisan dattawa, Kakakin majalisan wakilai da mataimakin kakakin majalisan wakilai kariya daga gurfana da kuma fensho har rayuwarsu ta kare.
Jaridar punch ta bada rahoton cewa farsfesa sagay yayi maganan me a ranar litinin 21 da watan yuni ,ya siffanta wannan samarwan a matsayin son zuciya kawai. Yace su na amsan albashi , me kuma sike bukata domin morewa rayuwa.
“ Saraki tsohon gwamna ne, shin bai amsan fensho a Jihar Kwara ne? wannan abun haushi ne kuma rashin sanin ya kamata; wannan kololuwan rashin hankali ne. Wannan na nuna cewan ba su tsoron yan Najeriya.Masu bukatan irin wannan su tambayi jama’a kafin suyi irin wannan. Zan fada wa Shugaban kasa yayi watsi da shi”. Sagay ya siffanta neman kariyan saboda su aikata kaifi sannan suyi ikirarin kariya.
“Har yanzu mutane na kukan me yasa aka Shugaban kasa da Gwamnoni kariya, wai kuma yanzu Senatoci ke bukatan kariya. Idan abun hakane ,yan najeriya su ce su ma a basu kariya kenan? Abun ya ban tsoro ace akwai masu irin wannan tunanin, wannan shirme ne”. Ya kara.
KU KARANTA: Babu kariya,babu fensho ga ‘yan Majalisa – SERAP,Falana
Senata shehu sani ya ce shi baya goyawa wannan samarwan baya: “Ni musamman ban yarda a baiwa yan majalisu , gwamnoni ko mataimakan su kariya ba”.
The post Akwai rashin hankali cikin san rai yan majalisa – Sagay appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.