Mugabe ya sa a tsare ‘yan wasan kasarsa na Olympics
-Shugaba Mugabe ya ba da umarnin ‘yan wasan olympics
-‘Yan wasan ba su ci komai ba a gasar wasannin
-‘Yan wasan za su biya kudin da aka kashe musu
Rahotanni na cewa Shugaba Mugabe na kasar Zimbabwe, ya ba da umarnin a tsare daukacin ‘yan wasan kasar da suka je gasar Olympics da aka yi a Rio ta kasar Brazil.
A cewar wani rahoto na gidan talbijin na NTA, Mugabe ya gana da shugaban rundunar ‘yan sandan kasar Agustine Chichuri, a inda ya bayar da umarnin a tsare tawagar ‘yan wasan da zaran sun sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Harare.
Zimbabwe ta aika da tawagar ‘yan wasa 31 a gasar mai farin jini ta duniya, amma na kusa da cin wani abu da wani dan wasa ya kai shi ne matsayi na 8 a dukkanin gasar wasannin da kasar ta shiga, takaicin hakan ne ya sa shugaban mai shekara 92 a duniya, ya ba shugaban ‘yan sandar kasar umarnin da ya kame su, ya kuma tsare.
KU KARANTA: Rio 2016: Nigeria ta karci kasa a tseren mita 100 na mata
An rawaito shugaban na cewa, ”mun kashe kudinmu a kan wadannan beraye wai su ‘yan wasa. Idan ka san ba za ka iya sadaukar da kai ka ci tagulla ko bakin karfe ba (matsayi na 4 da na 5), kamar yadda makwabciyarmu Botswana ta yi, dan me za ku sa mu barnatar da kudinmu a banza.” Robert Mugabe ya kammala da cewa, ‘yan wasan za su biya kudin da aka kashe musu ko da hakan zai dauki su shekara 10 su biya.
The post Mugabe ya sa a tsare ‘yan wasan kasarsa na Olympics appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.