Mayakan sojin sama na Najeriya sun saki bidiyo dauke da luguden wutar da suka yi wanda ya raunata Shekau.
-Mayakan sojin sama na Najeriya sun saki bidiyon da ke nuna harin da ta kai kwanannan a arewa maso gabas wanda ya raunata Abubakar Shekau sosai.
-A daren 19 ga watan Agusta mayakan sojin sama na Najeriya, sunce sun kasha yan ta’addan Boko Haram 300 a lokacin da suka kai harin ta sama.
-Bidiyon ya nuna harin daga sararin samaniya tare da lalata duk abunda ke wurin.
Mayakan sojin saman wato NAF sun saki wani bidiyon da ke nuna daya daga cikin manyan nasarorin yaki da ta’addancin da ake yi yanzu a arewa maso gabas. An saki bidiyon bayan da mayakan Najeriyar suka yi da’awar kasha yan ta’addan Boko Haram 300 a ranar da suka yi barin wutar ta sama wato ranar 19 ga watan Agusta.
An ruwaito cewar shugaban yan akidar wato Abubakar Shekau, ya jirkata sosai lokacin harin ta sama.
A yayin da ake cewa za suyi ganawa a wani wuri dake tsakanin Malam Fatori da wani wuri da suka maye a Kangarwa. NAF sun kuma saki wasu hotuna da ke nuna yakin saman da iya barnar da suka yi. Bidiyon wanda ya nuna barin wutar da suka yi bai nuna Shekau ba, ko wani daga cikin shugabannin Boko Haram da aka raunata. Kuma bai nuna adadin mutanen da aka kasha a harin ba.
The post Mayakan sojin sama na Najeriya sun saki bidiyo dauke da luguden wutar da suka yi wanda ya raunata Shekau. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.