Добавить новость
World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Boko Haram sun saka wuta a kauyen Borno; an sace mata

-Kungiyar Boko Haram sun kai hari wani kauye a jihar Borno sun kuma kwashe kayan abinci

-Yan ta’addan sun kuma sace mata

-An kashe mazaje bakwai (7) a harin

Alamu sun nuna cewa yakin kungiyar Boko Haram bai kare ba yayinda yan ta’addan suka kai hari wani kauye a jihar Borno, sun kuma kashe mutane bakwai. Bisa ga Sahara Reporters, harin ya faru ne a farkon ranar Asabar, 20 ga watan Augusta a kauyen Kuruburu dake karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

Wani dan banga ya bayyana cewa yan ta’addan sun mamaye kauyen kan Babura suna ta harbi ba kaukautawa. Sun kuma sace mata da kayayyakin abinci.

A halin yanzu, kungiyar masu goyon bayan Buhari a kafofin watsa labarai, sun aika da sako ga Iyayen yan matan Chibok da aka sace da kuma kungiyar BringBackOurGirls cewa karda suyi zanga-zanga kamar yadda aka tsara.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta zuba biliyoyin naira cikin tattalin arziki

Bayan sakin bidiyon da kungiyar Boko Haram tayi na kira ga sakin dakarunsu domin dawo da yan matan Chibok da suka sace, kungiyar ta bayyana shirin ta na yin zanga-zanga a fadar shugaban kasa.

Muhammad Labbo a wata sanarwa ya bukaci kungiyar da kada suyi zanga-zanga saboda hakan na iya rushe shirin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi na ceto yan matan.

The post Boko Haram sun saka wuta a kauyen Borno; an sace mata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus