ND Avengers sun zargi hukumomin tsaron ruwa da karya
– Neja Delta Avengers (NDA) sun zargi hukumar tsaro ta ruwa kan rashin iya aiki tare da karya
-Tsagerun, sun jaddada jarumancin su da kuma shirin su gagarumi nan gaba
-Sun gargadi NUPENG, PENGASSAN tare da baki ‘yan kasashen waje da su guji cibiyoyin mai dake Neja Delta
Neja Delta Avengers (NDA) ta karyata sanarwar da hukumar soja ta ruwa ta Najeriya ta bayar cewa ta kama wani babban dan kwangilar ta.
KU KARANTA : Yan sanda sun kama wani Fasto kan tsagerun Neja Delta
Mai magana da yawun ‘yan tsageran, Brig. General Mudoch, ya bada sanarwa cewa mutanen su na nan, kuma suna samun nasarar yaki. Yana mai cewa:
“Labaran da ke cewa, hukumar tsaro ta ruwan Najeria ta kama wani mai kaima Neja Delta Avengers kayayyaki babbar tatsunniya ce ta karni na 21. Hukumar bata iya kama kowa daga mutanen mu har sai mun durkusar da tattalin arzikin kasar
The post ND Avengers sun zargi hukumomin tsaron ruwa da karya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.