Gwamnati tayi Magana akan karatun addini a makarantu
–Ma’aikatar Ilimi ta yi Magana akan zancen hada karatun mabiya addinin Islama da na kirista.
– “Babu tilastawa a cikin addinan guda biyu”
Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin da akayi akan zancen karatun addinin islama da na kirista
Malam Adamu Adamu ,Ministan Ilimi ya bayyana matsayar gwamnati a wata jawabin da Mr. Ben Bem-Goong,mataimakan diraktan yada labarai ya bayar.
Game da cewar Jawabin, yan makarantun sakandare na da zabin su dauki kowani batu cikin guda biyun dangane da addinin su
Wata bangaren Jawabain tace : “Wannan umurnin ya zama wajibi saboda makonnin nan ana jin maganganu iri-iri akan cewa an mayar karatun islama da kirista bai daya. Babu tilastawa a cikin addin guda 2. Daliban sakandare na da zabin daukan duk wanda suke so daga ciki dangane da addinin da sukayi imani da shi.
Ilimin addinin islama da ilimin addinin kirista basu gushe suna cikin jarabawan daliban afrika ta yamma ba watau West African Examinations Council (WAEC) da kuma jarabawan yan najeriya kacal watau National Examinations Council (NECO).
Idan akwai wani canji na cewa an hada addinan biyu, West African Examinations Council (WAEC) da kuma jarabawan yan najeriya kacal watau National Examinations Council (NECO) zasu bayyana cikin ayyukan su da jarabawan su.”
KU KARANTA : Wajibi ne mu bunkasa ilimin ma’aikatan mu – Dambazau
A wannan makon, ma’aikatar ilimi ta sanar da soke jarabawan share fage shiga makarantun sakandaren gwamanatin tarayya.
The post Gwamnati tayi Magana akan karatun addini a makarantu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.