Gwamnoni sun gana a fadar Shugaban kasa
–Gwamnonin Najeriya za suyi hadaka da kamfanin Vodacom akan yadda za’a bunkasa bangarori a kasan nan
–Hakan ya bayyana ne bayan ganawar da sukayi a fadar shugaban kasa
Bayan ganawar bangaren zantarwa a ranar laraba,20 ga watan yuli, kungiyar gwamnonin Najeriya sunyi ganawa a Old Banquet Hall da ke fadar Shugaban kasa a Abuja.
wasu gwamnonin
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa anyi ganawan karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, misalin karfe 8 na yamma.
Gwamnonin da suka halarta sune gwanonin jihar Abiya, Gwambe, Neja, Bauchi ,Kebbi, Kaduna, Ogun, Delta, Sakkwato, Adamawa da Katsina. Gwamnonin da mataimakan su suka wakilce su sune gwamnonin Jihar Ribas, Imo, Barno, Ondo, Ekiti, Enugu, Cross riba,da Ebonyi.
Kungiyar gwamnonin Najeriya zasu yi hadaka da kamfanin vodacom a kan bunkasa kiwon lafiya,ilimi,da aikin noma a kasar. Tashar yada labarai ta Channels tv ta bada rahoton cewa gwamna yari yayi magana da manema labarai bayan ganawar ,yace yanada muhimmanci su samu goyon baya daga ma’aikatan da ake son a inganta.
KU KARANTA : Shugabancin Kasa : Yan Najeriya sun ki Atiku.
Anyi ganawar bayan ganawar majalisan farfado da tattalin arziki , majalisan na da aikin baiwa shugaban kasa shawara akan al’amuran da suka shafi tattalin arzikin kasa. Ta kunsa gwamnoni jihohi 36, gwamnan babban bankin tarayya da wasu mambobi karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
The post Gwamnoni sun gana a fadar Shugaban kasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.