Zaben Gwaman Ondo 2016: Sanata ya dau fom din APC
–Sanata Ajayi Boroffice ya dau fom din takaran gwamnan Jihar Ondo
–Zai yi takara karkashin jam’yyar APC
–Bayan daukan fom din,yayi wata ganawar asirce da shugaban jam’yyar APC ta kasa,John Oyegun.
Farfesa
Ajayi Boroffice wajen karban fom din
,sanatan da ke wakiltar mazabar Ondo ta kudu ,ya dau fom din takaran gwamna karkashin jam’yyar APC domin ya samu takara a zaben share fagen jam’yyar a Jihar Ondo. Ya dauki fom din ne ranan laraba,20 ga watan yuli, Wadanda suka taka mai baya sune uwargidan sa, Farfesa Olusinmibo, Hon. Babatunde Kolawole, dan majalisan wakilai; Rt Hon. Kenneth Olawale, tsohon kakakin majalisa dokokin Jihar Ondo; Dr Pius Osunyikanmi; Hon. Diran Iyantan,tsohon kwamishanan kananan hukumomi da sarakunan gargajiyan jihar Ondo.
Sauran ma’aikatan sa ne , barr. Ade Ajanaki, lauyan sa; Kayode Adeniyi Fakuyi,mai magana da yawunsa; Gani Muhammad,diraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zabe. Jim da kadan bayan amsan fom, ya gauraya ya gana da shugaban jam’yyar APC, Cif John Oyegun, a sakatariyan jam’yyar dake Abuja.
KU KARANTA : Fasto Osagie Ize-Iyamu bera ne – Oshiomole
Wa’adin gwamnan mai ci zai kare 23 ga watan fabrairu.
Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta ce za’a yi zaben ranar 26 ga watan nuwamba. A ranan lahadi 17 ga watan yuli, jam’yyar APC ta saki jadwalin yadda zata gudanar da zaben firamaren Jihar Ondo. Jam’yyar ta sanar da yadda za’a saya fom din daga sakatariyan jam’yyar daga ranan 19 ga yuki zuwa 5 ga watan agusta. Kuma za’a sayar da fom din a kudi N5 miliyan , yayinda zasu biya N15,000 kudin fom din nuna aniya.
The post Zaben Gwaman Ondo 2016: Sanata ya dau fom din APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.