Za’a dakatar da kasar Rasha daga gasar Olympics
Wata kotun sauraren karar harkokin wasanni watau Court of Arbitration For Sport (CAS) ta kori wata kara da kwamitin kula da harkokin gasar Olympics ta kasar Rasha ta gabatar a gaban ta tana kalubalantar hukuncin da hukumar kula ta harkokin wasannin guje-guje ta kasa-da-kasa watau International Amateur Athletics Federation (IAAF) ta yanke a kanta.
A baya dai ita hukumar ta International Amateur Athletics Federation (IAAF) ta kori kasar Rasha ne daga gasar ta Olympics bisa ga zargin shan kwayoyi masu sa kuzari da tace yan kasar tata suna anfani da su. Haka zalika ma kwamitin kula da gasar ta Olympics watau International Olympic Committee (IOC) yana nan yana duba yoyuwar dakatar da kasar daga gasar da za’ayi a cikin wata mai kamawa na Agusta a garin Rio na kasar Brazil.
Wani mai magana da yawun kwamitin yace: “Yanzu haka dai wasu mahukuntan kwamitin sun bayyana cewa yan kasar ta Rasha ba zasu yi tseba a gasar ta Olympics sakamakon samun su da akayi da laifin shan kwayoyi masu sa kuzari”.
The post Za’a dakatar da kasar Rasha daga gasar Olympics appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.