Добавить новость


World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

EFCC ta kama tsohon mataimakin kakakin majalisa

-Hukumar EFCC sun tambayi tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Bauchi, Sace Dumba sa wasu biyu

-An gayyacesu ne domin amsa tambaya kan kudin cin hanci naira milliyan 500

-Sun samu kudin ne daga hannun Garba Dahiru, tsohon kwamishinan kudi na jihar

Tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Bauchi, Hon. Sace A. Dumba, tare da wasu biyu sun amsa tambaya daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli. Sauran biyun sun kasance, shugaban karamar hukumar Dass, Mohammed Suleiman Rabo, da kuma tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party na karamar hukumar Dass, na jihar.

Sun amsa tambaya ne a ofishin kwamishinan Gombe kan zargin cewa suna da hannu, cikin rabon kudi kimanin naira milliyan 500 ga karamar hukumomi 20 na jihar, domin gudanar da zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shekara 2015, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sake fasalin al’amura ne kawai zai ceci Najeriya – Ekweremadu

Wata babban majiya a hukumar EFCC, ta ce an rahoto cewa an bayar da kudin ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, a karamar hukumomin jihar, daga Garba Dahiru, kwamishinan kudi,  a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Isa Yuguda.

A cewar majiyar, a lokacin amsa tambayoyin, sun yarda da cewa sun sa hannu kuma sun karba kudin da ake Magana daga hannun Garba domin kaiwa jam’iyyar PDP a dukkan karamar hukumomi na jihar.

The post EFCC ta kama tsohon mataimakin kakakin majalisa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus