Yan bindiga sun farma yankin okogbe a jahar ribas
A cewar Daily post, rikicin ya aukune a yankin okogbe a yammacin karamar hukumar ahoda a jahar ribas sakamakon yunkurin daukan fansa da yan bindigan suka jeyi wanda ya haifar da tashin hankali a jahar. Rikicin ya tursasama mutane shiga gidajen su domin tsira da lafiyan su.
Ance rikicin ya somane bayan da aka kashe wani mutum a ranar 19 ga watan yuni wanda aka bayyana da suna Ngozi obenne wanda ba’asan kosuwa suka aikata ba da misalin karfe hudu na safe. Acewar majiyan kashe mutumin ya janyo ramuwar gayyan da yan bindigan suka kai a yanki okogbe inda suka fara harbin mutane tako ina.
Babu takamaimai adadin mutanen da aka kashe, amman wata majiya da ba’a tabbatar ba tace guda tara aka kashe. Har yanzu ba’aji komai ba daga bakin yan sandan jahar ribas din.
Yan bindigan sun tsananta muguntar su a yankin Elegbete da Igbolomu ahirin ga watan yuni inda sukai ta shiga gidajen mutane da bayan daya suna musu fashi. Mutane 13 yan bindigan suka budema wuta inda suka same su a magudanun ruwan yankin Ikorodu.
The post Yan bindiga sun farma yankin okogbe a jahar ribas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.