– Wani kwamishin na hana almudahana take ci gaba da kama wadanda aka zargin laifukan cin hanci da rashawa
– Wani labari take fitowa ta bayyana wanda hukumar EFCC ta kama jigogin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) guda biyu saboda badakalar Naira Biliyan 23
Jaridar Rariya ta ruwaito wanda hukumar EFCC ta kama wani tsohon Gwamnan jihar Kaduna da dan takarar Gwamnan jihar Kano a zaben shekara da ya wice kan Naira Biliyan 23 na kudin zabe.
KU KARANTA KUMA: An bayyana akan kame-kamen hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta kama wani tsohon gwamnan jihar Kaduna mai suna Ramalan Muktar Yero da dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar PDP mai suna Salihu Sagir Takai.
An kama Takai da Yero ne a jiya Litinin, 16 ga watan Mayu, bisa zargin su da hannu a kudin yakin neman zabe, inda suka kwana a ofishin hukumar dake jihar Kano, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Haka kuma majiyarmu ta gano cewa sakataren jam’iyyar PDP na jihar Kano mai suna Alhaji Auwalu Ibrahim Dambazau, shi ma ya shiga hannun hukumar EFCC.
A yayin da hake jawabi kan lamarin, wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa suna kokarin ganin an bada belinsu.
Haka kuma Iliyasu Kwankwaso ya kalubalanci hukumar ta EFCC, inda ya zarge ta da yin zabe a mutanen da take kamawa. Ya kuma yi mamakin yadda ake tuhumar membobin jam’iyyar PDP kadai.
The post Badakalar Naira Biliyan 23: Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamna da dan takara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).