An buga kokarin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) data lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa na Asabar 5, ga watan Disamba domin magoyan bayan gwamna sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Nation ta ruwaito wanda wasu magoya bayan gwamna da masu biyayyan Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa sun zo yakin neman zaben yan adawa, jam’iyyar APC a filin kwallon kafan Samson Siasia a Yenegoa, birnin jihar Bayelsa a Talata 1, ga watan Disamba.
Wani labari tana bayyana wanda shuwagabannin jam’iyyar APC sun je Yenegoa saboda goyi bayan dan takarar jam’iyyar APC da kuma tsohon gwamnan jihar, Cif Timipre Sylva kamar yadda zai ci karo da gwamnan a zaben.
A filin yakin neman zaben, mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo shine ya wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari. Sannan akwai shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie-Oyegun da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Cif Bisi Akande.
Wasu gwamnonin a can, akwai Adams Oshiomhole (jihar Edo); Aminu Tambuwal (jihar Sakkwato) da mataimakin gwamnan jihar Imo.
Mataimakin shugaban kasa yace: “Lokacin canji ta zo. Lokacin na ci gaba ta zo.Lokacin na gwamnati mai kyau ta zo. Ku shiga wannan jirgin kasa (shine jam’iyyar APC). Abinda Shugaba Muhammadu Buhari yake so, shine ku shiga jam’iyyar mu, kamar muna da gwamnatin tarayya.
“Wannan jihar da mutanen ta, suna da girma. Amma, ku yi abun mai kyau. Abun mai kyau, shine ku fita PDP, da shiga APC. A yanzu, shine lokacin da ku fita PDP. A Asabar mai zuwa abun mai kyau zaku yi, shine ku samu katin zaben ku da jefa kuri’a na jam’iyyar APC.”
The post Matsala A Bayelsa: Magoya Bayan Gwamna Sun Koma APC Daga PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.