Wani mutum yaci dukan tsiya a hannun wata Karuwa inda hart a fasa masa kai da kwalba bayan yayi mata tayin biyanta kudin kwanciya da dafaffen kwai.
Wannan lamari mai daure kai ya faru ne a garin unguwar Mashonaland dake garin Mvurwi na kasar Zimbabwe.
Shi dai wannan Mutum dan rainin hankali sunan sa Moses Mushonga ya ji a jikinsa inda karuwar ta farfasa masa kai bayan ya saka hannu ya kama mata mama, sa’annan yayi tayin biyanta ladan kwanciya da yake son yi da ita da dafaffen kwai.
KU KARANTA:Ýansanda sun fasa ma karamar yarinya kai da bindiga
Ita kuwa karuwar mai suna Chipo data fahimci rainin hankalin Moses yayi yawa ba tayi wata wata ba inda ta dauki kwalbar giya ta fasa masa a kai, sa’annan ta dinga naushinsa a fuska har sai daya suma.
Ko da Moses Mushongo ya farfado daga doguwar sumar da yayi, jini ya cigaba da kwarara daga fuskarsa, nan ya sa kuka yana cewa “aid a tace bata yi kawai ya isa”
Karin haushi a wurin Moses Mushongo shine Ýansanda sunce ba zasu kama Chipo ba ko su gurfanar da ita gaba kotu, asali ma Ýansandan cewa sukayi matakin da Chipo ta dauka yayi daidai, don ta horar da shi yadda girmama mata.
The post Kilaki tayi masa duka kan zai biyata ladan kwanciya da dafaffen Ƙwai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.