Yan ta’addan Boko Haram sun kuma kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya B.U. Umar, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Majiyar sojoji tace an kai ma Laftanal Kanal kuma kwamandan bataliyan sojojin Najeriya 114, a safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba an kuma kashe shi a tsakanin Bita da Pridang.
“Abun hawarsa ta taka wani abu amma bai ji ciwo ba,” wata majiya ta bayyana wa jaridar Premium Times.
“Ya fito don duba abunda ya samu abin hawar tasa sannan ne yan Boko Haram suka bude wuta suka kuma kashe shi a wannan hali.”
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Sakkwato tayi makokin Dasuki
Ance sojojin na hanyarsu ta zuwa Yola a jihar Adamawa daga Bita a Borno lokacin da aka kai masu harin na bazata.
Kwanan nan Umar ya koma matsayin kwamandan tawagar sojoji 114 kimanin makonni uku da suka wuce.
A halin yanzu sojoji sun karyata masaniyar afkuwar abun ta kakakinsu Sani Usman, wanda yace bai da masaniyar mutuwar Laftanal Kanar Umar.
A halin yanzu, headkwatan hukumar tsaro ta karyata rahotannin cewa an biya wasu kudade kan sakin yan matan Chibok 21 da yan Boko Haram suka sake.
The post Labari da dumi-dumi: Boko Haram sun kuma kashe wani babban kwamandan sojoji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.