– Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana abinda ya faru tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
– Tsohon mataimakin shugaban kasar yace Obasanjo baiyi niyyar sauka daga mulki ba
– Atiku yace in da don ta Obasanjo ne, da ya maida ‘yan Najeriya bayi ya kuma ci gaba da mulki har abada
Tsohon mataimakin shugaban kasar,Atiku ya nace cewa Obasanjo yaso ya zama shugaba na din-din-din, ba wai yayi mulki karo na ukku ba kamar yadda mutane ke tunani ba.
Atiku ya fadi haka a wata hira da mujallar hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa mai suna zero tolerance .
KU KARANTA: Ta’aziyyar Buhari dangane da rasuwar Ibrahim Dasuki
The Punch ta ruwaito tsohon mataimakin shugaban kasar na cewa da farko ana tunanin cewa shirin na yima kundin tsarin mulki gyara ne yadda Obasanjo zai yi tazarce karo na ukku ko hudu. Amma a wayance an cire ka’idar yawan shekarun mulki yadda Obasanjo zai yi mulki na din-din-din.
Da aka tambayeshi dalilin da yasa yayi takin saka da Obasanjo wajen karshen mulkinsu sai yace, “Laifi na shine naki amincewa da gyaran kundin tsarin mulki yadda za’a cire kayyade yawan shekaru da yawan lokuttan zama kan mulki ko kuma abinda aka rika kira tazarce koko third term agenda.
“A bisa gaskiya, ya aiko ministan shari’a. na lokacin tare da Parfesa Jerry Gana wajena da gyaran da yake so ayi ma kundin tsarin mulki. Bayan na duba sai naga an cire kayyade lokacin mulki, a takaice yana iya mulkin har karshen rayuwarsa. Sai nace masu “idan na aike ku zaku iya kaima shugaban kasa wannan sakon? Sai suka ce e, sai nace “kuje ku gaya masa bana goyon bayan haka, kuma zan yaki manufar.”
Atiku yace dalilin wannan sabanin yasa Obasanjo ya lakafa masa cin rashawa.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post Yadda Obasanjo yaso ya cigaba da mulki har abada – Atiku appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.