– Mai shari’a Adeniyi Ademola zai fuskanci zargin laifukka 15 da gwamnatin tarayya (FG) ke masa – Matar Ademola, uwargida Olabowale Toluwatope Ademola zata fuskanci wasu daga cikin tuhumar da ake ma maigidanta – Laifukkan da ake zargin alkalin da matarsa kansu sun faru cikin shekarun 2014 da 2016 Mai shari’a Adeniyi Ademola na babbar […]
The post FG na tuhumar alkali Ademola da matarsa kan laifukka 15 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
– Mai shari’a Adeniyi Ademola zai fuskanci zargin laifukka 15 da gwamnatin tarayya (FG) ke masa
– Matar Ademola, uwargida Olabowale Toluwatope Ademola zata fuskanci wasu daga cikin tuhumar da ake ma maigidanta
– Laifukkan da ake zargin alkalin da matarsa kansu sun faru cikin shekarun 2014 da 2016
Mai shari’a Adeniyi Ademola na babbar kotun kasa dake shiyyar Abuja da matarsa, uwargida Olabowale Toluwatope Ademola zasu fuskanci tuhumar laifukka 15 da gwamnatin tarayya ke masu.
Takardar tuhumar na dauke da sa hannun wata babbar lauyan gwamnati ta ma’aikatar shari’a Hajara Yusuf wadda aka shigar gaban babbar kotun kasa ta birnin tarayya, cewar rohoton Vanguard.
KU KARANTA: Mutuwar Dasuki: Gwamna Tambuwal ya mai da martani
A takaice, gwamnatin tarayya na tuhumar Ademola wanda yana cikin manyan alakalan da hukumar tsaro ta farin kaya (DDS) ta kai samame gidajensu a ranakun 7 da 8 ga Oktoba, kuma matarsa tayi laifukka wadanda suka saba ma sashe na 8 na dokokin hukumar hana cin rashawa wadda aka kafa a 2011 da kuma sashen a 115 na dokar kasa.
Gwamnatin tarayya tayi amanna an aikata laifukkan cikin Febrairu 2014 da Yuni 2016. Ana zargin su da amsar N40 miliyan tsakanin ranakun 20’da 21 ga Febrairu 2014, da kuma wata N30 miliyan daga kampanin Joe Odey Agi and Associates tsakanin ranakun 11 da 26 ga Mayu 2015.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
The post FG na tuhumar alkali Ademola da matarsa kan laifukka 15 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.