-Shugaba Muhammadu Buhari na kasar Marokko a yanzu kuma ya halarci taron majalisar dinkin duniya akan canji, yanayi
Bisa ga maganganun da yake yaduwa akan zuwan shugaban Buhari kasar Marokko domin taron majalisar dinkin duniya akan canjin yanayi, Shugaba Muhammadu Buahari yayi bayani akan dalilansa na zuwa kasar da kuma dalilin da yasa yan Najeriya su damu da canjin yanayi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a kasar Marokko ne a daren litinin,14 ga watan Nuwamba. A wata gajeruwar jawabin da NAIJ.com ta samu a ranan talata, shugaba Buhari ta bada jerin dalilansa na zuwa taron:
KU KARANTA: Mutuwar Dasuki: Gwamna Tambuwal ya mai da martani
Domin rage tashin hayaki
“A yau zan gabatar da jawabi a bude taron majalisar dinkin duniya akan canjin yanayi #COP22. A jawabin, zan nanata jajircewan Najeriya wajen rage tashin hayaki da kashi 20 a shekarar 2030, kuma muna sa ran kaiwa kashi 45 da taimakon duniya ba baki daya.”
Rafin Chadi
“Mutane na tambaya cewa shin dan me Najeriya zata damu da canjin yanayi. Amsan shine abin rayuwan ne garemu. Rafin Chadi ta tsote da kashi 10 cikin shekarun da suka gabata, wannan ya shafin rayukan mutane sama da million 5.”
Yawan ambaliya
“A kasar mu, an samu yawan ambaliyan ruwan sama wanda yake damun mu tun shekarar 2012, inda ya shafi akalla mutane miliyan 2.”
A bangare guda, Shugaba Buhari ya amshi rahoton da zai fitar da Najeriya daga cikin matsin tattalin arziki a ranan litinin 14 ga watan Nuwamba.
Ku biyo mu a shfinmu na Tuwita: @naijcomhausa
The post Dalilai 3 na zuwan shugaba Buhari kasar Marokko appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.