Kungiyar Kwadago ta ja kunnen Shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin man fetur, ta kuma ce maimakon haka gara gwamnati ta bi sahun kudaden da a ka sace a ka fita da su ta karbo ta yi amfani da su.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Kwamared Ayuba Wabba ya nuna damuwarsa kan zantuttuka masu karo da juna da ke yawo a kafafen yada labarai daga kamfanin mai na kasa NNPC da jami’an gwamnati kan karin kudin mai.
Wabba ya ce, “Kwata-kwata ba ma goyon bayan kowane irin karin kudin mai dan har yanzu ba mu ga alfanun wancan da a ka yi ba, ko da ba a sabunta dokar mafi karancin albashi ba, idan a ka sake a ka kara kudin man, to hakan na nufin sake tsunduma ma’aikata da talakawa cikin wahala.
Bai kamata gwamnati ta kalle mu a banza ba, bai kuma kamata ta dauki juriya da hakurin da mutane su ka yi a banza ba. Dan za mu shirya zanga-zanga ta daukacin ‘yan kasa baya ga wasu halattattun matakai da za mu dauka dan kin amincewa da karin. Gwamnati na da bukatar duba yiwuwar yin kasa da farashin man na yanzu ba wani sabon kari ba.
KU KARANTA KUMA: Ra’ayi: Arewa da sauran gyara –Sheikh Gummi
Dokar da a ke amfani da ita ta mafi karancin albashi lokacinta ya kare. Kuma kamar yadda kuka sani tun tuni muka mika bukatar mu ta sabunta dokar amma gwamanti na jan kafa wajen duba bukatar tamu.
Ma’aikatan Najeriya da ‘yan fansho suna da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin mu. Saboda haka bai kamata su ci gaba da shan wahala ba. A bisa haka ne mu ke nanata kiranmu ga gwamnati da ta gaggauta sabunta dokar mafi karancin albashi.
Yayin da ya yabawa gwamnati wajen yaki da cin hanci da kuma kokarin tabbatar da shugabanci na gari a kasar mu, Wabba ya ce ya kamata yakin ya kara samun tsari sosai da dokoki masu karfi da za su taimaka masa ya dore. Ya na mai cewa, an bata sunan kasar mu da albarkatun ta ta hanyar kin hukunta wadanda su ka sace kudaden al’umma. Dan haka ba ma so a yi ta leko ta koma a yaki da cin hanci.
The post Wahalar ta isa haka –Shugaban kungiyar kwadago appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.