Добавить новость
World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

‘Yan Shia sun yi arangama da ‘yan sanda Kano (Hotuna)

– A wani labari da dumi-duminsa, wasu fusatattun ‘yan  kungiyar ‘Yan Shi’a  sun yi arrangama da ‘yan sanda a Kano a cewar Premium Times

– An rade-radin an hallaka wani dansanda yayin wasu ‘yan shi’a suka rasa rayukansu, an kuma datse babbar hanyar zuwa Zaria mai muhimmanci saboda hargistin 

Wasu membobin kungiyar Shia

Wasu mabiya mazhabin Shi’a a Kano sun yi arangama da ’yan sanda a ranar Litinin 4 ga watan Nuwamba shekarar 2016, ana kuma rade-radin cewa wasu su da dama daga cikinsu sun rasa rayukansu.

A Rahoton da kafar yada labarai ta PremiumTimes ta yada a shafinta na intanet ta ce, rahotanin da ta ke samu na nuna cewa, an yi arrangamar ne a tsakanin ‘Yan Shia’a da kuma ‘Yan sanda a wajen Kano daidai garin Tamburawa, kan Titin zuwa Zaria da yau din nan.

Rahoton ya kuma ce, an hallaka wani dan sanda, su ma ‘yan shi’an sun rasa rayukan ‘yan uwansu da ba san ko nawa ne ba, a yayin arangamar.

KU KARANTA KUMA: Shi’a: Jihohin arewa 5 da ka iya haramta tarukan addini

 

 

Rahoton ya ci gaba da cewa, wani mazunin yankin wanda ya shaida lamarin ya ce, ‘Yan sanda sun yi arangama ne da ‘yan Shi’an, a kokarinsu na hana wani tattaki da ‘yan Shi’an suke yi.

An kuma karo yawan jami’an tsaro yayin da hargitsin ya sa aka datse babbar hanyar ta gwamnatin tarayya da hade Kano da sauran manyan jihohin kasar ciki har da Kaduna, da Abuja, da kuma Lagos.

A ‘yan kwanakin nan dai, ‘yan kungiyar ta Shi’a sun matsa kaimi da zanga-zanga don neman a sako shugabansu Ibrahim Zakzaky wanda gwamnati ke tsare da shi.

‘Yan kungiyar sun kuma gudanar zanga-zanga a manyan biranen kasar ciki har da babban birin tarayya Abuja, inda yan sanda suka tarwatsa su da barko non tsohuwa mai sa hawaye.

The post ‘Yan Shia sun yi arangama da ‘yan sanda Kano (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus