Добавить новость
World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Rohr ya bukaci yan wasan Super Eagles su magance matsalar tsaron gida

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Gernort Rohr yace ya zama dole yan wasan Super Eagles su gyara tsarin bayansu idan dai suna so samu shiga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018 a kasar Rasha.

Rohr ya bayyana haka ne bayan wasan da aka fafata tsakanin kasar Algeria da Najeriya, inda Najeriya ta lallasa Algeria da ci 3-1.

Rohr ya nuna damuwarsa game da yawan ire iren daman cin kwallaye da masu tsaron gidan suka kyale Riyad Mahrez, da Yacine Brahimi suka dinga samu bayan an dawo hutun rabin lokaci. Matsalar da muka fuskanta kawai itace damammakin da Algeriya suka samu a sashi na biyun wasan, inji Rohr.

KU KARANTA:Gayyar sodi tayi sanadiyyar mutuwar matashi

Nasan abune mai wuya rike yan wasan Algeria, amma yan wasan mu masu tsaron gida sun nuna kwarewa. Sai dai ya bayyana cewar dole sai mun sake zage damtse musamman a bangaren tsaron gida.

Mikel da Victor Moses bayan cin kwallon su

Rohr ya cigaba da bayanin matsalar da Najeriya ke dashi musamman ta bangaren lamba Uku.

Muna da yan wasa masu buga lamba uku, sunyi kokari, amma dole ne mu tantance tsayayyen wanda zai dinga buga mana. Amma naji dadin sakamakon wasan.

A wasan daya gudana a filin wasa na garin Uyo, yan wasan Chelsea Moses Victor da Mikel Obi ne suka zura kwallaye Uku, inda dan wasan Algeria Nabil Bentaleb ya zura kwallo guda, hakan ya baiwa kasar Najeriya maki uku.

The post Rohr ya bukaci yan wasan Super Eagles su magance matsalar tsaron gida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus