Gwamna Amosun ya sallami shugabannnin NLC, TUC da NUT
– Gwamnatin jihar Ogun ta sallami Akeem Ambali da Dare Ilekoya shugabannin NUC da NUT
– Kana ta sallami wasu mambobin NUT guda 14 a jihar
– Wannan kora ya faru ne bayan ma’aikatan jihar Ogun suka tafi yajin aiki
Governor Ibikunle Amosu
Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun ya tabbatar da Koran shugabannin kungiyoyin kwadago ta NUC, NUT a jihar ta Ogun. Wannan kora ya faru ne bayan ma’aikatan jihar Ogun suka tafi yajin aiki kwana 11.
Akalla mambobin kungiyar gamayyar malamai NUT ne aka kora da kuma mambobin kungiyar kwadago ta NUC 16 sanadiyar rawan da suka taka na shirya taron ranan zagayowar malamai ta duniya a ranan 5 ga watan oktoba a ,Kuto,Abeokuta.
KU KARANTA: Hisbah ta kama karuwai 11 a Kano
Olusola Adeyemi,shugaban aikin gwamnatin jihar Ogun ne y sanar da Koran yace : gwamanti ta yanke shawara akan rahoton kwamitin bincike akan abubuwan da suka faru a ranan taron zagayowar ranan malamai da akayi a ranan 5 ga watan oktoba.
An ce shugaban NLC ya shirya wata zanga-zanga kua yayi maganganun batanci akan gwamnatin jihar wanda yayi iya tayar da tarzoma a jihar.
Saboda haka, gwamnatin jihar ta umurci dukkan ma’aikatunta ta kori wadanda suka taka rawa a ciki.
Yayinda wanda aka kora yaji hakan, yace : Babu wanda ya kira ni akan wannan batu kuma wannan yana nuni da azzalumin mulkin kama karyan da gwamnatin Ibikunle Amosun ta keyi.”
The post Gwamna Amosun ya sallami shugabannnin NLC, TUC da NUT appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.