Shugaban babbar asibitin tarayya ya shiga tsaka mai wuya
Kwamitin kuka da asusun ajiyar kudin al’umma na zauren majalisar wakila ta Abuja ya umurci shugaban asibitin tarayya dake katsina Federal Medical Center Dr Umar Faruk da ya gaggauta mayar da naira miliyan 2.7 zuwa asusun gwamnatin tarayya.
Doctors in ABUTH have begun indefinite strike
Kwamitin ya bayyana cewa asibitin bai da hurumin rike wadannan kudade a matsayin kudaden shigar su.
Shugaban kwamint danmajalissar wakilai dake daga jihar Ribars Kingsley Chinda da ya gabatar da kudurin ya bayyana cewa hukuncin da suka dauka sun yi amfani da wani ruhoto ne da suka samu a ofishin mai binciken kudi na gwamnatin tarayya.
Sai dai a martanin da Dr Faruk ya mayarwa ‘yanmajalissar ya bayyana cewa kudaden sun yi amfani da su ne wajen biyan kudaden da ake cazar asibitin da kuma sayen man injinan janareta domin amfani da kayan aikin dake cikin asibitin.
Saidai kwamitin binciken sun bukaci shugaban asibitin da ya gabatar masu da takardun shedar kashe kudaden kamin zaman da za su kara yi a ranar 8 ga watan Nuwamban da muke ciki.
The post Shugaban babbar asibitin tarayya ya shiga tsaka mai wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.