Wani yaro dan Najeriya ya farfado daga suma ya fara yaren sifanish
– Gaba dayan mu zamu yadda da cewa akwai abubuwa na mamaki da yawa da suke faruwa
– Iyayen wani yaro dan shekara 16 Reuben Nsemoh sun ga wannan a cikin ban mamaki
Nsemoh wanda yake rayuwa a US, ya samu mummunan rauni a kai a yayin da suke wasar kwallon kafa, wani yaro kuma da kuskure yazo ya kara fama shi a dai dai gurin a lokacin wasar 25 ga watan satumba, bayan kwallo ta kucce a kafar Reuben.
Ya farfado daga suman da yayi inda yake magana da yaren sifananci kamar jakin Kano a farko a cikin rayuwar shi,yana furta jimloli na sifananci wanda a da yan kalmomi kalilan ne ya sani na yaren kafin hatsarin.
“Nsemoh ya fada” na fara furtawa kawai, naji kamar shine baiwa da nake da ita ta 2, bana turanci na da kyau, kuma duk lokacin da nayi kokarin yin turanci sai inji na kasa, baiwa ne wannan, ba wani abun jin tsaro ba ne, ina matukar son haka, lalle wannan na musamman ne.
Duk da yake iyayen nasa sunyi mamaki, hakika ina cikin godiya tunda Reuben ya farfado, ban damu ba da yaren da yake yi, duk abunda ya faru ni dai tunda yana da rai kuma ya warke.
The post Wani yaro dan Najeriya ya farfado daga suma ya fara yaren sifanish appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.