Majalisar wakilai zata amince da bukatar Buhari ya amso bashin N12 triliyan
– Za’a amince da bukatar shugaba Muhammadu Bubari ya ciwo bashin $29.9 biliyan (N12 triliyan) domin ayyukan raya kasa na shekarun 2016-2019
– Majalisar dattawan na neman hanyoyin samun kudaden tafiyar da kasafin kudi na 2016 da kuma tsarin ciwo bashi na gwamnatin tarayya
President Buhari
Shugaban masu rinjaye Femi Gbajabiamila na bayani kan shirin majalisar na amincewa da bukatar shugaba Muhammadu Buhari na ya ciwo bashin $29.9 biliyan (kusan N12 triliyan) domin manyan ayyuka a shekarun 2016-2019.
An bayyana wannan labarin ga jama’a a wani buki a Lagos mai taken “canza rayuwa da goyon bayan jama’a” koko Changing Lives through Grassroot Support ranar Litinin 31 ga Oktoba.
KU KARANTA:Biafra: Minista ya shawarci masu fafutuka sunyi aiki da tsarin doka
Mista Gbajabiamila wanda ke wakiltar mazabar Surere 1 wanda kuma mamba ne na All Progressive Congress (APC), yace:
“Ciwo bashi domin tafiyar da ayyukan raya kasa ba aikin assha bane, jihar Lagos tayi haka kuma kowa yaga ci gaban da aka samu. Majalisar wakillan zata duba bukatar shugaban kasa domin ci gaban Najeriya kuma zata sa kwamitocinta su sa ido kan hukumomin gwamnati domin tafiyar da kasafin kudin 2016 kamar yadda doka ta tanada”
The post Majalisar wakilai zata amince da bukatar Buhari ya amso bashin N12 triliyan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.