Naira ta tsaya cak akan N470/$1 a kasuwannin canji
Darajan Kudin Najeriya Naira ya cigaba da kasancewa akan N470 ga dala guda a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba kwatankwacin darajarsa a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba.
Idan ba’a manta ba darajar Naira ya kara sauka bayan wasu yan satuttuka yana hawa, sakamakon karancin dala da aka samu a wannan lokuta.
Hakan ya faru ne duk da matakin da babban bankin kasa ta dauka na baiwa kamfanin Travelex lasisin umarnin cinikin dala a Najeriya, tare da bankin Fist Bank don siyar ma yan canji dala.
KU KARANTA:Nafi karfin inyi bara, inji Makaho mai siyar da cajan waya
Sai dai wasu yan kasuwan canjin sun ce har yanzu tsarin amfani da Travelex ya kasa wadatar da isashshen dala a kasuwanin canjin kasar nan. “bana samun isashshen dala daga Travelex” inji wani dan canji yake fada ma NAIJ.com.
Amma fa wasu masana harkar canji a Najeriya sun bayyana cewa ana sa ran a wannan sabuwar water, Naira zata kara daraja. Shugaban yan canji na kasa Aminu Gwadabe yace ana sa ran darajar zai karu ne sakamakon wasu manyan kamfanunuwar kasa da kasa zasu antayo dala cikin kasuwar.
“a yan kwanaki kalilan masu zuwa ana sa ran Naira zata yi daraja, sakamakon dala miliyan 2 da Travelex ta siyar a ranar alhamis daya gabata.” Inji Gwadabe.
Zaku iya duba ingantaccen farashin Naira a adireshin mu na yanar gizo NAIJ.com Bureau De Change.
The post Naira ta tsaya cak akan N470/$1 a kasuwannin canji appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.