Kotun daukaka kara ta ki yanke hukunci akan zancen PDP
– Wata kotun daukaka kara da ke zaune a Abuja taki yanke hukunci akan rikicin da ke faruwa tsakanin bangaroran PDP guda biyu
– Kotun tace hukuncin ta ya danganta da karan da aka kai wajen dayan Alkalin
– Jam’iyyar tace alkalan na san kai akan yanke hukunci akan al’amarin kotu
ali sherrif da makarfi
Kotun daukaka kara ta ki yanke hukunci akan al’amarin da ya shafi bangarorin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP guda biyu.
A zaman da kotun tayi a Abuja a yau,1 ga watan Nuwamba, kotun tace an dakatad da zancen har illa ma sha a llahu.
KU KARANTA: Biafra: Minista ya shawarci masu fafutuka sunyi aiki da tsarin doka
Kotun ta yanke shawaranta ne akan wata karar da ke kan Alkalai masu dubi cikin al’amarin.
Karar da jaridar NAIJ.com ta samu ya tuhumci Alkalan da laifin son kai a cikin al’amarin.
Har ila yau, bangaren Ali Modu Sherrif da Ahmed Makarfi na jam’iyyar PDP na sa’insa akan al’amarin shugabancin jam’iyyar ta adawa.
Tawagar Alkalan karkashin jagorancin Jumai Sankey tace an rigaya da an zubar mata da mutunci akan karar da aka shigar akanta.
The post Kotun daukaka kara ta ki yanke hukunci akan zancen PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.