Hisbah ta kama karuwai 11 a Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu yan mata masu zaman kansu, inda ta gurfanar dasu gaban kuliya a ranar Litinin 31 ga watan Oktoba.
Jami’an hukumar dake reshen karamar hukumar Fagge ne suka cika hannu da wadannan matan a unguwar Sabon Gari, jami’an sun kama su ne da zargin shan giya, shan wiwi da karuwanci.
Mata hudu daga cikinsu zawarawa ne, masu yaya, yayin da daya kuma ke dauke da ciki wata uku. An garzaya dasu gidan yarin kurmawa dake jihar Kano, inda zasu jira har zuwa ranar da za’a cigaba da sauraren karar, 14 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA: Jerin yan wasan Super Eagles da Rohr ya gayyata
Kwamandan Hisbah Salisu Umar yace “shekarun matan gaba daya bai wuce 21 zuwa 24 ba, mun kama su ne da tsakar dare a gidan giya na Faringida da na Abedie a Sabon Gari. Sa’annan mun gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo”
Salisu Umar ya bayyana laifukan da ake zargin matan da aikatawa a matsayin miyagun ayyuka, kuma ya jaddada cewa zasu cigaba da sa ido akan masu aikata ire iren laifukan nan.
The post Hisbah ta kama karuwai 11 a Kano appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.