Wani mutum ya canza sunan sa zuwa Iphone 7 kan wannan dalilin
Wani mutum ya canza sunan shi zuwa iPhone 7 saboda kamfanin yace duk mutum 5 da suka fara yin haka zasu samu kyauta.
Wani mutum dan kasar Russia wanda ya canza sunan shi gaba daya zuwa iPhone Sim ta samu kyauta ranar juma’a, lokacin da ake zantawa da shi yace sunan shi na ainahi Olexanda Turin, yace ze iya canza wa zuwa sunan in ya samu yara.
Yan uwan shi da iyayen shi sun tsorata da farko, daga baya kuma sai suka goya mai baya.
Yar uwar shi tace ba komai yana kokarin bayyana kanshi ne kawai.
“Duk wani mutum a duniya yana kokarin bayyana kanshi, dan me baze yi haka ta wannan hanyar ba, ta fadi haka dan ta kare dan uwanta kan abun da yayi.
Zaka iya yin abun da yayi?
The post Wani mutum ya canza sunan sa zuwa Iphone 7 kan wannan dalilin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.