– Gwamna Ayodele Fayose ya karyata amsar N5.7 biliyan domin zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi cikin 2014 daga wajen tsohon karamin ministan tsaro Musliu Obanikoro wanda a yanzu yake hannun EFCC
– Yace ba zai shiga kace- nace da EFCC ko Obanikoro ba
– Yace kafin yanzu Obanikoro ya aika ma EFCC da bakaken maganganu
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya karyata amsar N5.7 biliyan domin zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi cikin 2014 daga tsohon karamin ministan tsaro Musliu Obanikoro wanda ke hannun EFCC a yanzu.
A wata hira da yayi da Daily Sun, Fayose yace yana zargin EFCC da gwamnatin tarayya da kokarin ganin bayansa ta kowane hali. Yace ba zai shiga kace- nace da EFCC ko Obanikoro ba, ya kara da cewa kawo yanzu,’Obanikoro ya aiko ma EFCC da bakaken maganganu.
KU KARANTA: Jam’iyar PDP ta toshe jam’iyar APC a dandalin sadarwa
Ya Kara da cewa, Obanikoro na neman mafita ne daga matsalolin da yake ciki domin an kwace gidansa,an kuma rufe masa asussan ajiya na bankunan sa.
Kan ‘yan sandan shanu koko cow marshals daya kirkiro bada dadewa ba, gwamnan yace ba wai yaki jinin yin kiwo bane, yana kare manoma ne daga barnar da shanun ke yi masu.
The post N5.7 biliyan: Obanikoro na neman mafita – Fayose appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.