Добавить новость
World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Masu fafutukar ganin an kwato matan Chibok ta tozarta diyar Shugaba Buhari

Kungiyar nan mai fafutakar tirsasa gwamnati kan nemo da dawo da ‘yan matan Chibok wato Bring Back Our Girls BBOG ta zargi daya daga cikin ‘ya’yan Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Hadiza Buhari-Bello da amfani da sunan kungiyar wajen tattara kudade da sunan ‘yan matan Chibok din.

Kungiyar ta BBOG ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata, dauke da sa hannun jagororin kungiyar, Aisha Yesufu da Oby Ezekwesili da ke nesanta kanta daga wani taro da aka gabatar don kaddamar da asusun tallafawa ‘yan matan Chibok bisa jagorancin kungiyoyin “Peace Corps Of Nigeria” da kuma “Africa Support And Empowerment Initiative”. Kungiyoyin da ‘yar shugaba Buhari, Hadiza Buhari-Bello ke jagoranta.

BBOG ta bayyana kidimarta bisa yadda a wajen taron aka rangada tambarin kungiyar # BringBackOurGirls ba tare da sanar da su game da taron ko kuma neman izini ba.

KU KARANTA KUMA: Wasu Sojojin Najeriya sun bata

BBOG ta bayyana cewa ba ta da hannu ko masaniya da wannan taro na kaddamar da asusun tallafi ga ‘yan matan Chibok kuma ba da amincewar kungiyar aka yi amfani da sunanta ba. A saboda haka ta ke kira ga jama’a da su ankara da wannan shiri mai cike da alamu na zargi.

Kungiyar ta ci gaba da cewa “Bayan daukar tsawo kwanaki 902 muna fafutukar ganin an samo ‘yan matan, abin takaici ne wasu su yi amfani da wannan kokari namu wajen cimma wata manufa tasu”

“Mun samawa kanmu suna a idon duniya sakamakon aiwatar da tafiya tsakani da Allah ba tare da bin wasu don su bamu kudaden gudanar da ayyukanmu ba. Wannan shi yasa kungiyarmu ta ke kungiyar al’umma ba kungiyar wani ko wasu ba”

Mun kuma yi umarni ga lauyoyinmu, Femi Falana & Co da su dauki mataki akan wannan yunkuri da wasu ke yi don bata sunan kungiyarmu ta hanyar siyasantar da ita da mayar da ita hannun wasu ta yadda za a iya yin amfani da kungiyar da wata manufar ba manufar kafa ta ba.

Zuwa yanzu dai ba mu da tabbacin adadin kudin da aka tara a wancan taro”.

The post Masu fafutukar ganin an kwato matan Chibok ta tozarta diyar Shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus