Amurka na goyon bayan kokarin Bubari na gyaran tattalin arzikin Najeriya
– Jakadan Amurka a Najeriya mista Peter Barlerin, yace kokarin sarrafa tattalin arzikin Najeriya zuwa ga fitar da abubuwan da ba mai ba zai jawo hankalin Amurka da duniya wajen kayan
– Barlerin, na yaba ma kokarin Bubari nan gyaran halin tattalin arzikin Najeriya
– Jakadan na Amurka ya bayyana shirin kasarsa na kara cinikayya da saka jari a Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Amurka na yaba ma kokarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na sarrafa tattalin arzikin Najeriya zuwa ga wanda ba na mai ba.
KU KARANTA: ‘Yan matan Chibok 100 ba za su dawo ba saboda wannan dalili
Mukaddashin mataimakin sakatare mai kula da Afrika ta yamma kan tattalin arzikin yankin Peter Barlerin, ranar Talata 18 ga Oktoba yace sarrafa tattalin arzikin Najeriya zuwa ga wanda ba na mai ba zai jawo hankalin Amurka da sauran duniya.
Leadership ta ambato Barlerin na ambaton cewa Amurka na duba yadda zata kara zuba jari a Najeriya. Jakadan Amurka yace fara hako man shale da iskar gas cikin shekaru 10 da suka wuce ya canza tattalin arzikin Amurka inda bata dogaro da shigowa da mai balle daga Najeriya.
The post Amurka na goyon bayan kokarin Bubari na gyaran tattalin arzikin Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.