Matasa sun banka ma ofishin yan sanda wuta a Zamfara
Wasu matasa sun banka ma ofishin yan sandan kauyen Magazu dake karamar hukumar Tsafe wuta bayan samun sabani jama’an kauyen da yansandan.
Wani shedan gani da ido daya bukaci a sakaya sunansa ya fada ma kamfanin dillancin labarai cewa sabanin ya samo asali ne bayan wani mai laifi Ibrahim Muhammad dake kulle a ofishin yan sandan ya rasu.
KU KARANTA: Matar da mijinta ya datse mata hannaye, ta samu na roba
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Ibrahim ne sakamakon sace na’urar wayar tarho ne da yayi. A cewar majiyar, Mutuwar Ibrahim ne ya harzuka matasan yankin, inda suka tasan ma ofishin yansanda suka farfasa shi tare da banka masa wuta.
Shima Kaakakin rundunar yan sanda na jihar Shehu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin. Kaakakin yace tuni hukumar tasu ta fara tattara bayanin rahoton yadda lamarin ya kasance.
A wani labarin kuma, yan bindiga sun kashe yansanda uku a kan wani gari Hawan Kibo dake kan iyakan jihar Filato da Kaduna. Majiya daga hukumar yansanda tace yanbindigan sun yi awon gaba da makaman yansandan.
The post Matasa sun banka ma ofishin yan sanda wuta a Zamfara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.