Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta mayar da martani ga zargin cewa an fifita Kristoci a Najeriya fiye da Musulmai da kuma batun ranar Juma’a a matsayin hutu a kasar
Kungiyar Kristocin Najeriya CAN, ta mayar da martani ga kalaman Farfesa Ishaq Akintola shugaban Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeria MURIC na cewa, an fifita mabiya addinin Krista a kasar fiye da Musulmai, da kuma kiran a mayar da ranar Juma’a ranar hutu a kasar.
A rahoton jaridar The Punch, Babban Sakataren Kungiyar CAN, Musa Asake ya ce, ya ji takaicin cewa wadannan kalamai na fitowa daga wanda ya kai matstayin Farfesa a ilimi, sannan ya kuma ce, Akintola ba shi da masaniyya kan kundin tsarin mulkin kasar, bai kuma kamata ya yi magana kan wannan batun da ba shi ne a gaban kasar ba a yanzu.
KU KARANTA KUMA: A gurfanar da masu wa’azi dake sa kiyayar addini- Soyinka
Babban Sakataren ya kuma ce, batun cewa gwamnati na fifita wani addini kan wani, bai taso a yanzu ba, “Musulmai ya kamata su farka daga barcin da suke yi, su kuma yi gyaran cikin gida, ba Kristoci ba ne suka jefa su a halin kuncin da suke ciki ba, illa dai su tashi tsaye, su kuma cimma burinsu na rayuwa, ba zarge-zarge marasa tushe ba.”
A kwanan nan ne Asake ya yi ikirarin cewa, Musulmai na kokarin kawar da mabiya addinin Krista daga doron kasa a Najeriya, bayan da aka kashe matar wani fasto, aka kuma kai hari kan wani Cocin Katolika a cikin mako guda.
The post Ba a fifita Kristoci a Nigeria ba – Kungiyar CAN appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.