Majalisar dinkin duniya ta bayyana Najeriya a matsayin “kasar da babu hadin kai sakamakon bambancin kabila, addini da yanki, kuma da haka ne siyasar kasar take gudana.
An bayyana haka ne a wani taron tuntuba da na samar da tsarin gudanarwar na majalisar dinkin duniya don cigaban yankin kudu maso gabashin kasar nan a garin Awka.
Rahoton ya bayyana cewa a shekaru 10 da suka wuce, jama’a a yankunan kasar nan da dama sun nuna bacin ransu game da zargin wariya da ake nuna musu, zaluntar su, ko kuma nufin karar dasu. Rahoton ya kara da bayyana halin kakanikayi da kasar ke ciki sakamakon karancin ababen more rayuwa a kasar, sa’annan ya nuna babban matsalar dake damun kasar shi ne lalacewar tattalin arziki, rashin ababen more rayuwa da rashin sahihin shugabanci.
Wani sashen rahoton yace:
“Kasar Najeriya na daya daga cikin kasashe mafi talauci da kuma nuna bambanci, inda sama da mutane miliyan 80 a kasar talakawa ne.
“Yunwa da talauci sunyi kamari a yankunan karkara da kuma tsakanin iyaye mata a dukkanin fadin kasar.
“A yanzu haka tattalin arzikin kasar na cikin matsananci hali, ga shi kuma kudeden shiga na gwamnati ya ragu da kashi 33. “tabarbarewar tattalin arzikin ya sanya shakku a zukatan masu zuba jari game da farfadowarsa.”
Bugu da kari rahoton ya bayyana yawaitan cin zarafin mata da kanana yara, ciki harda matsalar fyade tare da bayyana adadin yan Najeriya matasa marasa aikin yi da suka kai kashi 42.
“A yanzu haka Najeriya na fama da matsaloli daban daban kamar su kwararowar Hamada, rikicin kabilanci, yakin bokoharam, ambaliyar ruwa, wuce gona da iri na jami’an tsaro.
“Sakamakon wannan yayi sanadiyyar zamar da jama’a da dama yan gudun hijira,” inji rahoton.
Rahoton ya bayyana cewa canja fasalin tattalin arzikin kasar nan na bukatan sabon tsari, ya bada shawarar gina mutanen kasa, tare da habbaka bagaren sarrafa kayan noma.
A satin daya gabata ne shugaban majalisar dinkin duniya ta sashin afirka Toby Lanzer ta kamanta matsalar da ake fama dashi a yankin Borno da irin abin da ke faruwa a kasashen da ake yaki. Lanzer ta bayyana hakan ne a yayin wani ziyara da ta kai Bama.
“Duba da yadda aikin da nayi a Darfur, Chechnya da kudancin Sudan, gaskiya ko a can iya abin da na gani kenan,” inji Lanzer.
A wani hannun kuma, kungiyar baiwa kananan yara agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya tayi gargadin yara sama da dubu 49 ka iya rasa ransu idan ba’a kawo agaji ba a yankin arewa maso gabas.
The post Majalisar dinkin duniya tace kan yan Najeriya a rarrabe yake appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.