Добавить новость


World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Yan sanda sun karbe sakatariyar jam’iyyar APC kan wannan dalili

– Jami’an yan sandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) babin jihar Ondo

– Yan sanda sunce han kai jami’ai sakatariyar APC domin hana karya doka daga wasu mambobi da wadanda ba mambobin jam’iyyar ba

– Shugaban jam’iyyar na jihar ya kuma ba da tabbacin cewa za’a gudanar da zaben zango na farko cikin lumana a ranar Asabar

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa baki daya, John Odigie-Oyegun

Jami’an Yan sandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar ALL Progressive Congress (APC) babin jihar Ondo.

Bisa ga rahoto daga jaridar Daily Sun, jami’in dan sanda dake kula da dangantakar jama’a (PPRO), Mr Femi Joseph yace an kai jami’an yan sanda sakatariyar domin su hana karya doka daga mambobi da wadanda ba mambobin jam’iyyar ba.

KU KARANTA KUMA: Fulani makiyaya sun kai hari ga Fayose kan dokar kiwon dabbobi

“Mutanen mu na gurin kuma zasu ci gaba da kasancewa a gurin har sai zaman lafiya ya dawo jam’iyyar. Bama son mutanen mu suyi amfani da wannan daman sabanin da ya shiga tsakanin yan jam’iyyar su tada rigima a jihar, saboda haka mun rigada mun bayyana dalilin da yasa mutanen mu suka kasance a gurin” Cewar sa.

Rahoton ya kara da cewa an dauke kayan asirin da aka ajiye a kofar shiga sakatariyar, yayinda sakatariyar jam’iyyar ta kasa baki daya suka sanya baki cikin rikicin.

KU KARANTA KUMA: Malami ya ba dalibinsa kyauta

A halin yanzu, shugaban jam’iyyar na jihar ya ba da tabbacin cewa zasu gudanar da zaben zango na farko cikin lumana a ranar Asabar.

Jam’iyyar ta kuma karyata labaran cewa ta cire shugaban ta, Hon Isacc Kekemeke, cewa jam’iyyar na karkashin kulawar Kekemeke kuma zai ci gaba da kasancewa haka har sai sakatariyar jam’iyyar ta kasa baki daya ta yanke shawara da ya saba da haka.

The post Yan sanda sun karbe sakatariyar jam’iyyar APC kan wannan dalili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus