Добавить новость
World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Magajin kwankwaso nayi masa bita-da-kulli

Majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta zartar da wani kuduri da ya nemi a soke sunan Kwankwasiyya daga gine-ginen gwamnati.

Majalisar ta kuma nemi a sauyawa rukunin gidaje da aka yi wa lakabi da Kwankwasiyya da Amana da kuma Bandirawo suna, a inda ta nemi da a sanya musu sunayen malaman addini. A zamanta na ranar Larabar nan, majalisar ta amince da a sanyawa rukunin gidajen Kwankwasiyya suna Shaikh Jafar Mahmud Adam.

Shi kuma rukunin gidajen Amana zai amsa sunan Shaikh Nasuru Kabara, a inda Bandirawo zai koma Khalifa Shaikh Ishaka Rabiu. Majalisar ta kuma ce a goge duka sunayen “Kwankwasiyya” daga jikin gine-ginen gwamnati, da aka rubuta a lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso ke gwamnan Kano.

Shugaban masu rinjaye na majalisar ta dokokin jihar Kano, Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya shedawa BBC cewa, sun dauki wannan mataki ne saboda bai dace a rinka rubuta sunan wata kungiyar siyasa a kan ayyukan gwamnati ba.

To sai dai wasu ‘yan majalisar kamar Zubairu Mamuda Madobi da ke goyon bayan Kwankwaso, sun ce ba sa goyon bayan matakin takwarorin nasu, kuma sun yi Allah-wadai da kudirin. Su dai suna ganin wannan wani bita da kullin siyasa ne ake yiwa Rabiu Musa Kwankwaso.

A baya-bayannan dai dangantaka ta yi tsami tsakanin gidajen siyasar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma wanda ya gada Rabiu Musa Kwankwaso.

The post Magajin kwankwaso nayi masa bita-da-kulli appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus