An cire wa bankin UBA takunkumin haramcin cinikayyar kudaden waje
Babban bankin Najeriya, CBN, ya cike bankin UBA daga cikin jerin bankunan da ya hana su hada-hadar kudaden waje, saboda bankin ya mika kudaden NNPC da ke hannunsa.
Wata sanarwar da CBN ta fitar ta ce dage haramcin a kan bankin na UBA zai fara aiki ne a ranar Alhamis.
Tun da fari dai CBN ta hana bankuna tara yin dukkan hada-hadar da ta shafi amfani da kudaden kasashen waje, har sai sun mika kudaden asusun kamfanin mai na kasar, NNPC da ke hannusu zuwa asusun bai daya na gwamnatin tarayya.
Masu sharhi a kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan matakin.
The post An cire wa bankin UBA takunkumin haramcin cinikayyar kudaden waje appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.