Добавить новость


World News in Dutch


Новости сегодня

Новости от TheMoneytizer

Ganduje zai share kwankwasiya a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar goge kwankwasiyya a jihar bayan wani kuduri da wani dan majalisa ya gabatar

Ganduje da Kwankwaso a lokacin ana dasawa

Rahotanni na cewa a zamanta na ranar Laraba 24 ga watan Agusta, Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar da ta lamincewa gwamnatin jihar a karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta goge duk wani wuri da aka rattaba sunan Kwankwasiya a fadin jihar.

Kudurin dokar wacce Hon Baffa Babba Dan Agundi, mai wakiltar karamar hukumar Birni ya gabatar, rahotannin sun ci gaba da cewa, an tafka muhawara a kanta a yammacin ranar, kafin ta samu amincewar mafi rinjayen yan majalisar, daga baya ta zama doka.

KU KARANTA: Gwamnan Kano ya kafa tarihi a Arewa

Bisa wannan doka, gwamnatin jihar za ta cire kalmar Kwankwasiyya a duk inda aka rubuta a wurare mallakar gwamnatin jihar, musamman gine-gine da kuma sauran wurare na jama’a, su ma rukunin gidaje na Kwanksiyya da Amana za a canza musu suna zuwa na wasu fittatun malamai a jihar.

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa kwankwaso ne ya fito da tsarin rubuta  Kwankwasiyya a duk ayyukan da gwammatinsa ta yi a jihar, a inda a waccan lokaci gwamnan ya ke cewa, ya yi hakan ne domin gudun runton aiki, hakan ta sa aka rubuta kalmar a ko’ina, kama daga jikin  katangar makarantu da rufinsu, zuwa hanyoyi da gadoji, har da fiyip-fayip na ruwa da gwamnatin ta yi oda daga kasar waje.

A martanin tsohon gwamnan wanda kuma aka rika yadawa a shafukan sada zumunta da muharawa na Facebook, Rabiu Musa Kwankwaso ya na mai cewa, iya abinda za’a iya yi ke nan, amma ba‘a isa a rusa su ba, gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, shi ne mataimakin Kwankwaso a tsawon shekaru takwas da ya yi na mulki a karo na daya da na biyu.

 

 

The post Ganduje zai share kwankwasiya a Kano appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Читайте на сайте


Smi24.net — ежеминутные новости с ежедневным архивом. Только у нас — все главные новости дня без политической цензуры. Абсолютно все точки зрения, трезвая аналитика, цивилизованные споры и обсуждения без взаимных обвинений и оскорблений. Помните, что не у всех точка зрения совпадает с Вашей. Уважайте мнение других, даже если Вы отстаиваете свой взгляд и свою позицию. Мы не навязываем Вам своё видение, мы даём Вам срез событий дня без цензуры и без купюр. Новости, какие они есть —онлайн с поминутным архивом по всем городам и регионам России, Украины, Белоруссии и Абхазии. Smi24.net — живые новости в живом эфире! Быстрый поиск от Smi24.net — это не только возможность первым узнать, но и преимущество сообщить срочные новости мгновенно на любом языке мира и быть услышанным тут же. В любую минуту Вы можете добавить свою новость - здесь.




Новости от наших партнёров в Вашем городе

Ria.city
Музыкальные новости
Новости России
Экология в России и мире
Спорт в России и мире
Moscow.media










Топ новостей на этот час

Rss.plus