Gwamnatin Jihar Bauchi ta kwace filin Raymond Dokpesi
–Cif Raymond Dokpesi na daga cikin yan takaran kujaran Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa
–An bada rahoton cewa gwamnatin jihar bauchi ta kwace filin kamfanin Daar Communication
Takardan zantar da kwace filin, kwamishanan filaye ,Alhaji Abubakar Tatari Ali ya sa hannu.
Takardan tace : “Ina mika maka wannan sako cewa an cire sunanka daga filin saboda cin zarafin al’umma kamar yadda yak e cikin sashe na 28 na dokokin amfani da fili.”
An tattaro cewa kwamitin tattara kadarorin jihar bauchi ta ziyarci filin inda gidan Talabijin na AIT da gidan rediyon Raypower ke zaune. Kwamitin ta fada wa ma’aikatan cewa za a dau irin wannan mataki.
Manajan AIT na Jihar Bauchi, Yakubu Bala,ya bayyana cewa kwace filin ya shafi wata shiri da gidan rediyon ke yadawa wacce ta tsananta ma gwamnatin.
KU KARANTA : Dan majalisar Kano, Jibrin ya roki aiki ta kafar yada labarai.
Mai kamfanin gidan talabijin da rediyon da aka kwace ma fili, Raymond Dokpsei yana takaran shugaban Jam’iyyar PDP, kuma ana goya masa baya hardu su Attahiru Bafarawa,tsohon gwmanan jihar Sokoto.
The post Gwamnatin Jihar Bauchi ta kwace filin Raymond Dokpesi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.