Jami’ar Soja ta kashe kanta
A jiya Laraba 24 ga watan agusta ne jami’an filin tashin jirgi na kasa da kasa dake kasar Kenya mai suna ‘Jomo Kenyatta international Airport’ suka tsinci gawar wata jami’ar a daya daga cikin kewayensu.
Alamu na nuna cewa Sojar ta harbe kanta ne a ka. Tsintar gawar ke da wuya, sai fargaba ya cika mutanen dake cikin filin tashin jirgi.
a cewar shafin yanar gizon kasar Kenya, Sojar ta garkame kanta ne a daya daga cikin makewayan da yansandan filin tashin jirgin ke amfani da shi, daga nan ne sai aka ji karar harbin harsashi.
Sai dai haryanzu yansandan jihar kasar Kenya sun ki suyi bayani a hukumance dangane da afkuwar lamarin, amma akwai wasu labaran dake nuna cewa jami’ar sojan ta dade tana cikin damuwa da gajiya. Rahoton yace “wahalan aiki yasa ta kashe kanta”.
A wani labari kuma, wata sanarwa daga ofishin gwamnan birnin Turkiyya ya bayyana cewa sama da mutane hamsin (50) ne suka rasa rayukansu lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tashi bom a bainar jama’a yayin wani bikin aure a kudancin birnin Gaziantep.
Lokacin da shugaban kasar Turkiyyan Recep Erdogan yake tsokaci dangane da lamarin, yace wannan aikin yan ta’ddan kungiyar ISIS ne.
The post Jami’ar Soja ta kashe kanta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.