John Kerry ya gana da daliban Najeriya
Ziyarar da sakataren kasar Amurka John Kerry ya kawo kasar Najeriya ya kara armashi yayin da ya samu ganawa da wasu dalibai mata yan kasar Najeriya bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
mataimakiyar sakataren kula da nahiyar Afirka Linda Thomas tare da John Kerry
An zabo daliban ne daga bangarorin Fasaha, ilimin kere kere da lissafi inda suka gana da Kerry a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.
John Kerry ya tattauna batun Bokoharam da tsaro yayin ganawarsa da shugaba Buhari da Gwamnoni. Sa’annan ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yaki da almundahana da yake yi, kuma yayi alkawarin taimaka masa ta wannan fannin.
The post John Kerry ya gana da daliban Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.