Soyinka ya fada ma ya canza salon gwamnatinsa
–Wole Soyinka yayi wata ganawa da yan jarida akan ganawar da yayi da shugaban kasa Buhari a makon da ya gabata
–Farfesan ya bada shawaran cewa gwamnatin tayi kokarin samar da zaman lafiya a yankin Neja Delta.
–Ya kuma yi Allah wadai da ayyukan Boko haram
Farfesa Wole Soyinka ya kalubalanci gwamnati da ta kara yunkirin samar da zaman lafiya a yankin Neja Delta.
Soyinka ya nemi Shugaba Buhari da yayi hankali wajen kula matsalolin yankin mai dumbin arzikin mai. Yayinda yake Magana a hirar da yayi da yan jaridar a Jihar Legas,yace gwamnatin Buhari bata zange dantse wajen kula da matsalolin hayaniyar yankin Neja delta.
Wole Soyinka yayi kira da gwamnatin tarayya da ta canza salon gwamnatinsa kuma yayi gaggawan kawo sauyi kan matsalolin yankin Neja Delta.
Farfesa Soyinka yayi Allah wadai da ayyukan boko haram a yankin arewaacin kasan .Ya bayyana cewa ta’addanci na faruwa ne sanadiyar rashin hankali kuma ana bukatan a tsananta karfi.
Soyinka yace dole ne a fitittiki yan boko haram saboda basuda hankali. Farfesan ya gana da shugaban kasa muhammadu buhari a fadar shugaban kasa kuma yayi alkawari da cewa zai gabatar da wata hira da manema labarai akan ganawar.
KU KARANTA : Niger Delta Avengers sunyi barazanar fallasa sojoji
Maganganun Soyinka na zuwa ne a wata lokacin da yan bindiga a yankin neja delta keyi na kai hare-haren bam a kafufuwan man fetur. Wadannan ayyukan sun durkusar da fitan man najeriya da ganga 700,000 a rana daga 1.56 million a rana. Wadanda suka fi shahara sune Tsagerun Neja delta Avengers.
The post Soyinka ya fada ma ya canza salon gwamnatinsa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.