Saraki ya kyautata mahaifiyar Reshidi Yekini (Hotuna)
Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya ceto mahaifiyar marigayi Rashidi Yekini daga kangin fatara kuncin rayuwa bayan ya gyara mata gida da kuma samar mata wasu kayyakin jin dadin more rayuwa
Rashidi Yekini a lokacin ya na tashe a duniya
Sanata Bukola Saraki tsohon gwamnan jihar Kwara, kuma shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje mahaifiyar marigayi Reshidi Yekini da abubuwan inganta rayuwa.
Mama Yekini and late son
Sanatan ya gyara gidan da take da zama, tare da farfado mata da ‘yar sana’ar tireda da ta ke yi.
Hotunan mahaifiyar marigayi Rashidi Yekini fitaccen dan wasan kwallon kafa da yayi suna a lokacin ya na raye ya bazu a kafofin yada labarai a inda jama’a suka tifa albarkacin bakinsu dangane da halin da tsohuwar ta ke ciki bayan mutuwar dan taa shekarar 2012, wanda ya na daya daga cikin wadanda suka fito da sunan kasar a kwallon kafa a duniya.
The post Saraki ya kyautata mahaifiyar Reshidi Yekini (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.