Mutane 4 sun mutu a hadarin mota a titin Jihar Edo
–Wata mumunan hadrin mota ya faru a Jihar Edo
–Kimanin mutane 4 ne suka rasa rayukan su a hadarin
–Hadarin ya faru a babban titin Benin
Kimanin mutane 4 ne aka ruwaiton cewa sun rasa rayukansu a wata mumunan hadarin motan da ya faru a Jihar Edo. Hadarin motan ya faru ne a babban titin da ke tsakanin Agbor na jihar delta da UPPer Sakpona ,Benin a ranar talata misalign karfe 5:30 na yamma.
Jaridar Daily Post ta bada rahoton cewa wani mutum wanda ake kyautata zaton cewa direba ne, yana ta kuwa cikin azaba.
A bangare guda, wani mutum daya ya rasa ransa a ranar laraba 24 ga watan agusta yayinda wata tankan man fetur ta tashi a Upper Mission junction a babban titin Benin-Auchi a karamar hukumar Ikpoba-Okha ta Jihar Edo.
Tashin wutan wanda ya faru misalign karfe 7 na safe ya bar mutane akalla 4 da rauni . an kuma bada rahoton cewa wutan gobaran ya hallaka dukiyan miliyoyin naira.
KU KARANTA : Wani gini a Jami’ar Kano ya auko,da alamar anyi rashi rayuka
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa akalla gidaje 4 ne suka kone sanadiyar gobaran wutan. Wata majiya a wurin ta bada rahoton cewa hadarin ya kashe mutane da yawa duk da cewa ba’a ambaci yawan mutanen da suka mutu ba.
The post Mutane 4 sun mutu a hadarin mota a titin Jihar Edo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.