Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello na cikin farin ciki biyo bayan hukunci da wata kotun daukaka kara ta yanke a ranar alhamis 3 ga watan agusta, inda tayi watsi da karar da James Faleke ya shigar yana kalubalantar zabensa da aka yi a matsayin gwamnn jihar Kogi. Alkali mai Shari’a Jummai Sankey tace kamar yadda […]
The post Yahaya Bello yayi farin cikin samun nasara a kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello na cikin farin ciki biyo bayan hukunci da wata kotun daukaka kara ta yanke a ranar alhamis 3 ga watan agusta, inda tayi watsi da karar da James Faleke ya shigar yana kalubalantar zabensa da aka yi a matsayin gwamnn jihar Kogi.
Alkali mai Shari’a Jummai Sankey tace kamar yadda sashi na 221 na kundin tsarin mulki ya tanadar, duk wani kuri’a da aka kada na jam’iya ne. alkalin ta kara da cewa karar da Faleke ya shigar ba tad a makama. Tayi bayanin cewa tsarin mulki bai yarda da wani yayi takara ba ba a karkashin inuwar jam’iya ba. Don haka Faleke ba shi da hurumin ikirarin mallakan kuri’un da aka kada kafin rasuwar Prince Abubakar Audu, kuma kafin a kammala zaben.
An hangi hotunan gwamnan tare da hadimansa suna cikin annushuwa. Ga kadan daga cikin su.
Idan ba’a manta ba, shi dai Faleke shine mataimakin dan takarar gwamnan jihar Kogi Prince Abubakar Audu a zaben da ya gudana a watan nuwamba na shekarar bara. Inda bayan rasuwar dan takaran ne hukumar zabe ta bayyana zaben a matsayin wanda ba’a kammala ba.
Bayan hakan ya faru ne sai hukumar zabe ta umarci jam’iyar APC da ta fitar da sabon dan takara da zai maye gurbin Abubakar Audu, a haka ne aka zabi Bello, wanda hakan bai yi ma Faleke dadi ba.
The post Yahaya Bello yayi farin cikin samun nasara a kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.